Kididdigar da shahararriyar jaridarnan ta kasar Amurka dake fitar da shahararrun masu kudin Duniya, Forbes ta yi ta
shekarar 2019, ta bayyana cewa har yanzu, Aliko Dangote ne wanda ya fi kowane bakar fata kudi a Duniya.
Akwai bakar fata 13 a jerin sunayen da Forbes din ta fitar kuma 'yan Najeriya hudu ne a cikinsu.
Na daya shine Dangote wanda ta bayyana cewa ya samu kudunshine daga harkar siminti, sikari, da filawa, sannan
Dangoten yana gina kafariyar matatar mai wadda idan aka kammalata zata rika tace danyen mai ganga 6500,000 duk
rana.
Dangote na da kudi da suka kai zunzurutun dalar Amurka
biliyan 10.9
Na biyu a jerin shine me kamfanin sadarwa na Glo da kamfanin hakar mai na Conoil watau Mike Adenuga wanda shi
kuma yake da zunzurutun kudi har dala biliyan 9.1
Na uku kuma shime Abdulsamad Rabiu me kamfanin BUA dake da zunzurutun kudi dala biliyan 1.6
Sai ta hudunsu itace Folorunsho Alakija, wadda itace mace ta farko a Najeriya da ta zama Biloniya, tana zunzurutun kudi
har dala biliyan 1.1
Ga cikakkun sunyen kamar yanda Forbes ta wallafa:
Aliko Dangote – Nigerian ($10.9 billion)
Mike Adenuga – Nigerian ($9.1 billion)
Robert Smith – American ($5 billion)
David Steward – American ($3 billion)
Oprah Winfrey – American ($2.5 billion)
Strive Masiyiwa – Zimbabwean ($2.4 billion)
Isabel Dos Santos – Angolan ($2.3 billion)
Patrice Motsepe – South African ($2.3 billion)
Michael Jordan – American ($1.9 billion)
Michael Lee-Chin – Canadian ($1.9 billion)
Abdulsamad Rabiu – Nigerian ($1.6 billion)
Folorunsho Alakija – Nigerian ($1.1 billion)
Mohammed Ibrahim – Sudanese-British ($1.1 billion)
No comments:
Post a Comment