Newssplash90

NEWS | SPORTS | CELEBRITY GIST | MIXTAPE | COMEDY VIDEOS | JOKES | TECH | FASHION

PROMOTE MUSIC | ADVERTISE | SUBMIT FREEBEAT

  • KARANTA SAQON AMINU ALAN WAKA ZUWA GA ADAM A ZANGO BAYAN KAMMALA ZABE



  • Tauraron mawakin Hausa, Aminu Alan Waka ya aikewa da abokin aikinshi, Adam A. Zango da sako na musamman bayan
    kammala zaben shugaban kasa da aka yi a makon jiya.

     Ga sakon kamar haka:

    Ina tuna Abubuwa da yawa da suka hadamu da kai Adamu kama daga kalmar shahada da yaren Hausa da zama a yanki
    daya ga Uwa Uba Sana'a Iri daya.

     Ina tuna haduwarmu a tarukan zumunci na waka ko Dandalin karbar kambum
    karramawa da makamantansu.

    ina tuna yanda mutane ke harsashenmu tamkar uwa daya uba daya dun abinda ya
    sameka ai ta bugo waya ana so a ji dahir daga gareni don zaton ni da kai abu daya ne, Saboda Sana'ar Waka.

    Me zai sa muga baiken juna a yayin da ra'ayinmu ya banbanta a kasuwar
    Bukata?

    Ina taya ka jaje na tallar abinda ka dauko baka kai ga nasara ba, Kuma ina yi maka bushara da hakuri da wautar masu
    wauta.

    Ina karfafa tunaninka da yabawa musamman yarda ka bayyana fatan Alkhairi ga wanda Allah ya baiwa Nasara.

    Akarshe Ina fatan zamu hadu karkashin kishin kasarmu Nigeria kasa Daya Al'umma Daya.

     Mu kuma dawo fagen Fama na
    Sana'armu don gani wanne tudu wanne gangare zamu kai ga ci, Don cigaba da Samarwa kanmu Mafita a harkar taro sisi.

    Allah ya baiwa kasarmu zaman lafiya da bunkasar arziki, ya baiwa shugabanmu jagoranmu lafiya da nisan kwanan da zai
    waiwayemu da ayyukan cigaba a arewa.
    Ameen.

    No comments:

    Post a Comment