Newssplash90

NEWS | SPORTS | CELEBRITY GIST | MIXTAPE | COMEDY VIDEOS | JOKES | TECH | FASHION

PROMOTE MUSIC | ADVERTISE | SUBMIT FREEBEAT

  • GARBA SHEHU YACE ANYI WA KALAMAN SHUGABAN KASA MUHAMMADU BUHARI MUMMUNAR FAHIMTA



  • Kalaman da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yi na cewa duk wanda ya saci akwatin zabe “ya yi hakan ne a bakin ransa,” sun haifar da ka-ce-na-ce a fagen siyasar kasar.

    Buhari ya bayyana hakan ne a wajen wani taro da jam’iyyarsa ta APC ta shirya a Abuja.

    Tuni jam’iyyar adawa ta PDP ta bayyana furucin a matsayin salon mulkin “kama karya,” tana mai cewa hakan zai sa
    dakarun kasar su rika daukar doka a hannunsu.

    “Komai za a yi a bi kundin tsarin mulkin kasa, abin da kundin tsarin mulki ya ce shi ne, idan an samu mutum yana laifi a
    kamo shi a tuhume shi.” Inji daya daga cikin jagororin da ke yi wa Atiku Abubakar kamfe, Malam Umar Sani.

    Sai dai kakakin shugaban kasar, Malam Garba Shehu, ya ce an yi wa shugaban mummunar fahimta, “saboda halin da ake ciki na siyasa.”

    “Hakika Shugaba Muhammadu Buhari gargadi yake yi ga ‘yan banga da masu zuwa suna kwatar akwatin kuri’a su gudu da su don su je su dangwala hannu a yi cuta.” Inji Garba Shehu.

    Garba ya kara da cewa, ana yawan samun irin wannan matsala a yankin kudancin Najeriya, dalilin kenan da ya sa a ja kunne.

    “Saboda haka, in an dauka ana ba shi wata ma’ana cewa ya yi
    a yi harbi, ai akwai doka.” Inji Garba Shehu.

    No comments:

    Post a Comment