Newssplash90

NEWS | SPORTS | CELEBRITY GIST | MIXTAPE | COMEDY VIDEOS | JOKES | TECH | FASHION

PROMOTE MUSIC | ADVERTISE | SUBMIT FREEBEAT

  • ILLOLIN HARSHE





  • Tabbas daga cikin dukkan gabobin da suke jikin 'Dan Adam, babu mafi saurin jefa mutum acikin kogin hallaka kamar HARSHEN SA.

    - Harshe wata tsoka ce wacce babu Qashi acikinta.

    - Amma tana ruguza kowanne irin Qashi agangar jikin mutum baki dayansa.

    - Harshe yakan iya warware Imanin dake Qulle azuciyar Dan Adam har ya mayar dashi kafiri ba tare da ya sani ba.

    - Harshe yakan janyowa gangar jiki Bulala, ko jifa, ko kuma sara da kansakalin takobi..

    - Harshe yana iya warware Soyayya ko abokantaka ko dangantaka da ta dade.

    - Harshe yakan janyo Fushin Allah akan mai shi.

    - Harshe yakan janyo ma mutum mummunar cikawa babu Imani.

    - Harshe yakan janyo akifa Mutum arika jansa akan fuskarsa acikin wutar Jahannama saboda miyagun abinda ya furta.

    - Harshenka kamar mafadacin zaki yake gareka. Idan ka barshi a 'daure ka tsira. Amma idan ka sakeshi sai ya fara hallakaka kafin ya hallaka duk wanda ka turashi zuwa gareshi.

    Saboda maganin wadannan illolin ne har da ma wasu, shi yasa SHUGABAN HALITTA (saw) yake cewa:

    "Duk wanda ya kasance yayi imani da Allah da ranar lahira, to ya fadi alkhairi ko yayi shuru".



    1 comment: