Newssplash90

NEWS | SPORTS | CELEBRITY GIST | MIXTAPE | COMEDY VIDEOS | JOKES | TECH | FASHION

PROMOTE MUSIC | ADVERTISE | SUBMIT FREEBEAT

  • KADAN DAGA CIKIN AMFANIN DA LALLE YAKE YI


  • Ga wasu hanyoyi kadan da ake amfani da lalle:

    -  Na farko dai lalle Kariya ce daga sihiri, Kariya ce daga aljanu sannan kuma Kariya ce daga cututtuka da dama.

    - Yin lalle a kafa na zuqe cutar dake kafa sannan yana maintaining dumin mace, bi ma ana yana inganta ni’imar mace ba tare da ya gushe ba.

    - Ga duk mace mai infection, ta tafasa lalle in ya dan huce sai ta yi sit bath dashi na sati biyu in Allah ya yarda zata warke.

    - Ana iya sha ruwan lalle cokali 1 don wankin dattin ciki amma banda masu ciki.

    - Don gyaran Fata; lalle dai ba karamin tasiri yake dashi wajen gyara fata ba, domin shi natural toner ne wanda ba bilicin yake yi ba amma yanasa haske mai kyau kuma yana goge dattin fata.

    - A bangaren gyaran fuska, tana sa fuska tai kyalli, laushi, da haske in an kwaba da ruwan Kwai amma banda kwaiduwar kwan,ki kwaba ruwa ruwa amma ba sosai ba ki lizimci shafa shi kaman sau uku a sati yayi kaman minti 20-30 kafin wanka sai Kinga bambanci a cikin sati biyu.

    - Ga masu son hasken fata, ki kwaba lalle da ruwa, ki shafe a jikinki inya bushe ki dirje da man zaitun za kiga canji.

    - Ga masu fama da pimples, yar’ uwa ki hada lemon tsami da lalle kwabi mai dan tauri amma ba sosai ba kina shafa wa a fuskar ki bayan watanni kuraje zasu mutu sannan tabo bazai zauna ba ga hasken fuska da laushi.

    - Sannan gamai son kamshin fata,
    Ki kwaba lalle da turaren ki mai kyau na ruwa wanda ake durawa ki zuba isasshen ruwa a bokati ,ki sa garin lalle ta jika tai já zir sai ki tsiyaye ruwan ki diga turaren ki mai kamshi ciki ,Bayan kinyi wankan sabulunki sai ki dauraye jikinki dashi inkin lizimci haka to bake ba rabo da kamshin jiki.

    No comments:

    Post a Comment