Shugaban hukumar zabe ta Nigeria wato Professor Mahmud Yakubu ya nemi afuwar yan Nigeria a bisa dage zabe da aka yi.
An dage babban zaben shekarar 2019 ne sa'o'i kalilan kafin fara shi, inda aka dage shi zuwa ranar 23 ga watan Fabrairun
shekarar 2019.
Wani darakta a hukumar zaben kasar Festus Okaye ya ce har bayan karfe 12;00 na daren ranar Asabar hukumar tana da
tabbacin za ta iya gudanar da zaben.
Jami'in ya ce sun samu matsala ne akalla a bakwai daga cikin jihohi 36 da ke fadin kasar.
Mista Festus ya ce hukumar zaben ta yi takaicin abin da ya faru kuma saboda haka tana neman afuwa daga 'yan kasar.
Daga nan ya ba da tabbacin cewa hukumar zaben ta dukufa wajen ganin ta gudanar da zaben kamar yadda aka tsara a mako mai zuwa.
Ya bukaci 'yan kasar da su ba hukumar goyon baya don ganin ta gudanar da sahihin zabe.
Mutane da dama ne suka rika bayyana rashin jin dadinsu da matakin da hukumar ta dauka na dage zaben a ranar Asabar,
musamman a kafafen sada zumunta.
Shin kai/ke meye ra'ayin ku bisa wannan lamari.
No comments:
Post a Comment